Mai dad'i, kuma dad'in wannan lada ya mantar da shi d'acin hak'urin da yayi cikin mawuyacin halin da ya tsinci kansa. 7. Daukar shawarar da Annabi (s.a.w) ya bayar a ingataccen hadisin nan yana daga cikin abubuwan da suka fi komai amfani a wannan fage. Ga dai abinda yake cewa: "KU RIK'A LA'AKARI (A ABUBUWAN DUNIYA) DA WAD'ANDA KUKA FI, BA DA WAD'ANDA SUKA FI KU BA; DOMIN WANNAN SHINE BABBAN ABINDA ZAI HANA KU RIK'A GANIN ALLAH BAI YI MUKU WATA NI'IMAR KIRKI BA". Bukhari da muslim ne suka rawaito shi. Don hak'ik'a idan bawa ya sanya wannan mahimmin ma'aunin a ransa zaka ga duk yadda yake, yafi mutane da yawa lafiya da arzuki da abubuwan da suke da alak'a da su. Ta haka sai damuwa,bak'in ciki da k'uk'umi da suke nema su kai shi k'asa sun gushe, farin cikinsa kuma ya k'aru, yayi ta murna, ganin cewa ya zarta matane da yawa a ni'imomin da Allah yayi musu gaba d'aya. Kuma a duk lokacin da mutum yayi zurfin tunani a kan ni'imomin da Allah yayi masa, na fili da na b'oye, da na addini da na duniya,to lallai zai ga ubangiji ya ba shi alheri ba kad'an ba,ya kuma kare shi daga sharruka masu yawa. Ba shakka irin wannan yana ije bak'k'an ciki, yana kuma sa zuciya ta yi fari fat; ta cika da farin ciki. FASALI (3) 8. Daga cikin abubuwan da suke kawo farin ciki, su kuma gusar da bak'in ciki da k'uk'umi, k'ok'arin gusar da ainihin abinda ya janyo wannan bak'in cikin, da kuma dogewa wajen samar da abubuwan da ke kawo farin cikin na farko dai ya san cewa abin da kawai ya wuce ya wuce, kuma ya sani cewa yana daga wauta da hauka da rashin aikin yi ya zauna yayi ta tunani a kan wannan abinda ya same shi, tunda dai aikin gama ya gama. Don haka ya daure yafi k'arfin zuciyarsa ya daina tunani akan abin, ya kuma yi k'ok'ari ya daina damuwa da sak'e sak'en zuciyarsa take masa na abubuwa da suka shafi rayuwarsa ta nan gaba, kamar ta rik'a masa cewa ta yiwu talauci ya same shi, ta yiwu wani abin tsoro ya afka masa, da dai shauran irin abubuwan da mutum yake tsoron su same shi a rayuwarsa ta duniya. Ya san cewa ba wanda ya san abinda zai faru nan gaba sai Allah, kuma duk abinda zai kasance a wannan lokaci mai zuwa na alheri ko na sharri,mai dad'i ko mara dad'i a hannun Allah yake Buwayi Gagara misali, Mai matuk'ar hikima a duk abinda ya hukunta. Abin da kawai bayi suke iya yi su yi k'ok'arin ganin sun samu alheri dake cikinsa, sun kuma ije sharri da ya k'unsa. Kuma bawa ya san cewa matukar zai daina fargaba da sannu damuwa akan makomar rayuwarsa, ya mik'awa ubangiji al'amarinsa yana mai nutsuwa da fatan ya rufa masa asiri, matuk'ar zai yi haka, to zaka ga zuciyarsa ta nutsu,kuma abubuwa sun dai daita, bak'in ciki da damuwa kuma sun kama gabansu. 9. Daga abinda yake kan gaba, yin wannan addu'ar da Annabi(s.a.w) shi da kansa ya kasance yana yinta, wannan addu'a kuwa itace: YA ALLAH KA GYARAMIN ADDINI NA WANDA SHINE K'ASHIN BAYAN AL'AMURANA,KA KUMA GYARA MIN DUNIYATA WADDA A CIKINTA ABINCINA YAKE, KA GYARAMIN LAHIRATA WADDA NANCE MAKOMA,KA SANYA RAYUWA K'ARIN DUK WANI ALHERI NE A GARENI, MUTUWA KUMA HUTU CE A GARENI DAGA DUK WANI SHARRI" (Muslim ne ya rawaito shi). Haka nan wannan addu'a: YA ALLAH DA RAHAMARKA KAD'AI NAKE SA RAI, DON HAKA (INA ROK'ON) KAR KA BARNI DA KAINA DAI DAI D K'IFTAWAR IDO, KA KUMA GYARA MIN GABAD'AYAN AL'AMURANA, BA WANI ABIN BAUTAWA DA GASKIYA SAI KAI".(Abu Dauda ne ya rawaito shi da isnadi ingantacce). Idan har bawa ya tara hankalinsa wuri guda, yayi da gaske, yayi ta yin addu'a ba k'ak'autawa kan Allah ya gyara masa makomar rayuwarsa ta addini da ta duniya, ya kuma tashi tsaye kan ganin hakan ya tabbata, to Allah kuwa zai cika masa burinsa, kuma bak'in cikin da ya dame shi ya koma farin ciki. FASALI(4) 10. Daga cikin abubuwan da suka fi komai amfani wajen gusar da damuwa da bak'an ciki, idan mutum ya tsinci kansa a cikin masifu k'ok'arin yaga ya rage musu k'arfi. Yadda zai yi kuwa shine: ya d'auka cewa halin da zai samu kansa a ciki a nan gaba, kuma idan hakan ta faru ga yadda zai yi ya daure,ya shanye wannan abu. Idan yayi haka,sai kuma ya ba da k'ok'ari wajen ganin sauk'ak'a abin da zai yi na halin da ya samu kansa a ciki daidai gwargwado. To sakamakon waccan dauriyar da yake shirin yi, da wannan k'okarin da yake yi a yanzu, sai kaga bak'k'an cikinsa sun gushe, maimakon haka kullum k'oka'rinsa shine ya samarwa kansa abubuwan da za su amfane shi, da maganin wad'anda zasu cuce shi, matuk'ar basu fi k'arfinsa ba. Idan abubuwan da suke haifar da tsoro, ko cutuka,ko talauci suka afka masa ko kuma ya rasa wani abu daga cikin ire iren abubuwan da yake so, to ya fuskance su cikin nutsuwa da dauriya. Kai yama yi shirin ko da sun fuce yadda yake tsammani ga irin juriyar da yake shirin yi, domin mutum ya sab'awa kansa da dauriya akan abubuwan k'i kan gusar da tsanani da yake k'unshe a cikinsu, ya kuma ji sun zo masa cikin sauk'i, musamman ma idan ya shagaltar da kansa da yak'arsu matuk'ar iyawarsa. Sai kaga ga dauriya, ga tashi tsaye akan abinda zai amfane shi duk sun had'u.

No comments: