HANYOYIN DA SUKE KAIWA ZUWA GA KYAKKYAWAR RAYUWA

Wannan misalin kuwa shine: hak'ik'a shi dai addini yana kira da babbar murya cewa kowa ya zama yana da wadatar zuci, dangane da arzuki, falala da karimci iri iri da Allah ya raba ya bawa kowa. Ka ga dai shi mumini gaskiya,idan aka jarrabeshi da rashin lafiya ko talauci da makamantansu daga cikin abubuwan da ka iya samun kowa sai ka same shi warkan ba abinda ya dame shi, saboda imaninsa, da wadatar zucinsa da yardarsa da abinda Allah ya bashi. Baya hank'oron abinda ba 'a k'addara masa ba. Yana duban wanda yake k'asa da shi, baya duban wanda ke sama da shi. Kai watakila ma sai kaga farin ciki, walwala, da watayawar da yake ciki ya kere wanda ya samu dukkan abubuwan da yake nema na duniya matuk'ar dai ba a bashi wadatar zuci ba. Kamar yadda zaka samu shi wannan da ba ya tafi da ayyukansa bisa doron imani, idan aka d'an jarrabe shi da talauci, ko rashin wani abin da yake so na duniya, sai ka same shi cikin wani irin tashin hankali da mummunan hali. Ga k'arin misali: idan aka shiga halin tsoro, ko kuma wasu rigimgimun duniya suka yi wa mutum ca, sai kaga mai ingantaccen imani ko a jikinsa. Gabansa ko faduwa ba yayi, gashi a nutse, yasan duk yadda zai b'ullowa wannan lamari da ya tinkaro shi da duk abinda Allah ya hore masa na tunani da magana da aiki, ya daure wannan abin tashin hankalin da ya afka masa. La shakka irin wad'annan ta'adu na hutar da mutum, su kuma tabbatar masa da zuciya. Kamar yadda zaka samu wanda bashi da imani, kwata kwata ya sab'a da wancan. Da wasu ababan tsoro sun faru duk sai ya bi ya canza, hankalinsa ya dugunzuma, tunaninsa ya tarwatsa, ya cika da tsoro da tararrabi, ya shiga cikin tsoro da damuwar da basu misaltuwa. Ire iren wad'annan mutane in basu da wasu d'abiu na halitta da za su taimaka musu, duk sai kaga sun fita daga cikin hayyacinsu, duk sun bi sun k'are sun lalace; saboda basu da imanin da zai hak'urtar dasu musamman ma a cikin da ke sa mutum ya kasa zaune ya kasa tsaye. Mutumin kirki da fajiri, da kuma mumini da kafiri, dukkanninsu suna tarayya wajen koyon jarumta da kuma yadda zasu sauk'ak'awa kawunansu ababan da ake gudun afkuwarsu. Sai dai mumini ya fita daban; saboda k'arfin imaninsa da hak'urinsa, da tawakkalinsa ga Allah,da kuma dogaronsa gareshi,da kuma neman lada a gareshi. Duk wad'annan abubuwa ne da jarumtarsu zata k'aru ta hanyarsu, za kuma ta sauk'ak'a masa tunanin bak'in ciki da sauran masifu. Kamar yadda Allah ta'ala yace: "IN HAR KU(MUMINAI) KUNA JIN RAD'AD'I TO SUMA (KAFIRAI) SUNA JI KAMAR YADDA KUKE JI, KUMA KU KUNA SA RAN SAMUN ABINDA SU BASA SA RAN SAMUNSA A WAJEN ALLAH(WATO ALJANNA)". (Nisa'i 104) kuma kaga suna samun taimako na musamman daga Allah mad'aukaki, wanda zai tarwatsa musu duk wasu ababan da suke tsoro. Allah Ta'ala yace: "KUMA KUYI HAK'URI, DON HAK'IK'A,ALLAH YANA TARE DA MASU HAK'URI". (Anfal 46). {2} Hakanan daga abubuwan da suke gusar da bakin ciki da damuwa : kyautatawa mutane da furuci ko da aiki, da dai sauran nau'o'in kyawawan ayyuka da ta'adu. Dukkannin wad'annan abubuwan alheri ne da ihsani,kuma duk wanda yake aikatasu mutumin kirki ne ko mutumin kawai, za a kare shi daga bak'an ciki iya gwargwadon yadda yake kyautatawa bayin Allah. Sai dai mumini zai rabauta sama da kowa, kamar yadda yake bambanta da cewa shi kyautatawarsa don Allah yake yi da kuma neman sakayyarsa. Sai Allah ya sawwake masa kyawawan ayyuka saboda alherin da yake fatan samu (daga Allah) ya kuma kareshi daga abubuwan da yake k'i saboda ihilasinsa,da neman sakayyarsa daga Allah(shi kadai). Allah Ta'ala yana cewa: "BABU ALHERI A CIKIN YAWANCIN GANAWAR DA SUKE YI IN BANDA WANDA YAYI UMARNI DA SADAK'A KO WANI KYAKKYAWAN AIKI,KO SASANTAWA TSAKANIN MUTANE. KUMA DUK WANDA YA AIKATA WAD'ANNAN ABUBUWAN(DA AKA AMBATA) TO ZAMU BASHI LADA MAI MATUK'AR GIRMA".(nisa'i 114) kaga sai Allah Ta'ala ya bayyana cewa ba wata tababa gabad'ayan wad'annan abubuwa da aka ambata alheri ne daga duk wanda suka fito. Kuma (aikata) alheri,alheri yake kawowa,ya kuma kad'e sharri.kuma lallai duk muminin da ke neman sakayyarsa a wurin Allah to ba shakka Allah zai bashi lada mai matuk'ar girma. Wani daga cikin jimillar wannan babban lada shine gushewar bak'in ciki da abubuwan da ke gurb'atawa mutum rayuwa da makamantansu. FASALI{2} 3. Daga cikin abubuwan dake zama riga kafin damuwa da tashin hankali da yawan tunani akan rigingimun duniya, mutum ya shagalta da kansa da wani aiki ko wani ilmi mai amfani; saboda wannan zai d'auke masa hankali daga tunani akan wannan abinda yake nema ya dagula masa lissafi. Kai ta haka ma watakila sai ya manta da abubuwan da suka janyo masa wannan bak'in ciki da tashin hankali, sai ransa yayi fari, kuma karsahinsa ya k'aru. Wannan sababin har walau mumini da wanda ba mumini ba sunyi tarayya a cikinsa,sai dai shi mumini ya sha bamban da sauran , saboda imaninsa,ihilasinsa, da kuma ladan da yake sa ran samu a wajen Allah lokacin da ya shagalta da kansa da wannan ilimin da yake koya ko yake koyarwa, ga shi kuma abinda ya sani na alheri yana