Yana aikata shi; idan wannan abu ibada ne kaga shike nan, in kuma wani aiki ne na duniya,ko wani abu da ya riga ya zama jiki sai kawai yayi shi da niyya ta gari yayi nufin cewa wannan abu yin sa ne don ya samu karsahi wajen bautar ubangiji. Wannan kuma yana da matuk'ar tasiri wajen ije bakin ciki. Sau tari zaka ga mutum an jarrabeshi da damuwa, da tab'arb'arewar al'amura sakamakon haka kawai sai kaga cututtuka iri iri sun afka masa kuma kaga ba wani magani da zai fi masa amfani irin yayi watsi da wannan abin da ya janyo masa damuwa, ya kuma gurb'ata masa rayuwa, da kuma shagaltar da kansa da wani aiki da yasa a gaba. Kuma zai yi kyau ace aikin da zai d'auke wa kansa hankali da shi dama yana daga cikin ayyukan da yake sha'awar yi, don haka ne zai sa kwalliya tafi biyan kudin sabulu. Allah shi yafi kowa sani. 4. Daga cikin abubuwan da ake maganin fargaba da damuwa da su,mutum ya tara tunaninsa wuri guda, ya mayar da hankali akan aikin da yake gabansa a wannan rana,kuma ya cire damuwa da abinda zai zo gaba,ko bakin ciki akan abinda ya shud'e,don haka ne Annabi (s.a.w) ya nemi tsari da Allah daga 'Fargaba' da 'bakin ciki' saboda shi bak'in ciki yana kasancewa ne akan abubuwa da suka riga suka wuce kuma ba dama a sake dawo da su ko kuma a cimmasu. Shi kuma 'Fargaba' yana kasancewa ne sakamakon tararrabi akan abin da zai zo nan gaba. Don haka ya kamata mutum ya zama aikin da yake gabansa shi kawai yasa a gaba,ya tara k'arfin bara da na bana, ya kuma ja d'amara wajen ganin ya gyara ranar da ya wayi gari da kuma lokacin da yake ciki, domin tara hankali wuri guda yana sa ayyukan da aka sa gaba su kammala,kuma mutum yana jin dad'i da haka sai kaga mutum ya sami saukin wannan fargaba da bak'in ciki. Annabi (s.a.w) ya kasance duk lokacin da zai wata addu'a ko zai nunawa Al'umarsa ita sai kaga yana yin k'aimi kan cewa a rik'a neman taimakon Allah da kuma kwad'ayin falalarsa, k'ari akan k'ok'arin da jan d'amara da mutum zai yi don ganin abinda yake so ya tabbata, kuma ya rabu da abinda yake rok'on a kawar masa. Saboda ita addu'a gwame take da aiki, don haka shi dai bawa ya rik'a yin k'ok'ari cikin abinda zai amfane shi a addininsa da duniyarsa, kuma ya rik'a rok'on ubangijinsa kan ya cika masa burinsa,ya kuma rik'a neman taimakonsa akan hakan. Kamar yadda Annabi (s.a.w) yace: "RIK'A YIN KWAD'AYIN ABINDA ZAI AMFANEKA, KA KUMA NEMI TAIMAKON ALLAH, KAR KUMA KA KARAYA, IDAN KUMA HAR WANI ABU YA SAMEKA TO KAR KA CE: 'KAGA KUWA DA ABU KAZA NAYI, AI KUWA DA ABU KAZA DA KAZA NE ZAI KASANCE'. ABINDA ZAI CE KAWAI SHINE: HAKA ALLAH YA K'ADDARA, KUMA ABINDA YASO SHI YAKE AIKATAWA'. DON KUWA ITA ' DA NA SANI' AYYUKAN SHAIDAN TAKE BUD'EWA". Muslim ne ya rawaito shi. Sai Annabi (s.a.w) a wannan hadisin ya had'a tsakanin umarni da ya bayar kan a rink'a kwad'ayin aikata abubuwa masu amfani a kowane lokaci, a kuma rik'a neman taimakon Allah,kar kuma mutum ya bari rauni ya shige shi, ta hanyar kasala da son jiki,ya kuma bayyana cewa a sallamawa hukuncin Allah da k'addararsa a cikin abubuwan da suka riga suka shud'e. Ya kasa abubuwan zuwa gida biyu: kashi na farko,mutum zai iya samar da shi,ko ya samar da wani b'angare na cikinsa,ko kuma ya hana shi faruwa,ko ya sauk'ak'a shi in ya aukun ire iren wad'annan abubuwa mutum zai iya yin iya bakin k'ok'arinsa, ya kuma nemi taimako daga ubangijinsa. Kashi na biyu kuma haka bazata yiwu ba. A irin wannan yanayi sai mutum ya kwantar da hankalinsa ya yarda ya kuma mik'a wuya ga hukuncin ubangiji. Ba wani kokwanto lallai la'akari da wannan babban ginshik'i yana kawo farin ciki, ya kuma gusar da fargaba da bak'in ciki. 5. Daga cikin manyan abubuwan da suke sa mutum ya ji fes a ransa yawaita ambaton Allah don wannan yana da tasiri mai ban mamaki wajen mutum yaji ba abinda yake damunsa, kuma fargaba,da bak'in ciki da suka sa shi a gaba sun gushe. Allah Ta'ala yace: KOWA YA KASA KUNNE YAJI: DA FA AMBATON ALLAH NE ZUCIYOYI SUKE NUTSUWA". Anbaton Allah yana da matuk'ar tasiri wajen samun wannan abin nema a karan kansa, ga ladan da bawa zai samu na ambaci ubangijinsa. 6. Hakananma ambaton ni'imomin da Allah yayi wa mutum, na sarari da na b'oye, domin ik'irari da ni'imomin ubangiji da yayata su, suna sa Allah ya ije wa mutum fargaba da bakin ciki kuma suna zaburar da bawa akan godiyar Allah, wannan kuwa shine matsayin da yake gaba da kowanne, domin ko da bawa yana cikin talauci ko rashin lafiya ko wani bala'i daga cikin bala'o'i, idan ya kwatanta da ni'imomin da Allah yayi masa wad'anda saboda yawansu ko k'irguwa baza suyiba, da kuma wannan abin k'in da ya same shi sai yaga ina da gami! Bara ma kaji: Idan Allah ya jarrabi bawa da masifu da abubuwan da yaso, shi kuma bawan ya dangana ya mik'a wuya, ya kuma yarda da halin da ya samu kansa a ciki, sai kaga masifun sun zo masa da sauki, ya kuma samu yadda zai yi. Kuma tunanin d'imbin ladan da zai samu tare da jin cewa hakuri,da yarda da hukuncin da Allah yayi yana cikin wata ibada ne ga Allah Ta'ala kan musanya masa mummuna da mai

No comments: